ALAMOMI GUDA SHIDA NA DAREN LAILATUL QADR


ALAMOMI GUDA SHIDA NA DAREN LAILATUL QADR
Daren lailatul qadri yana da alamomi da ake gane shi da su, wadannan alamomi suna kasancewa ne a cikin daren karan-kansa:
1- Dare ne mai haske, babu zafi ko sanyi a cikin sa.
An karbo daga Jabir Dan Abdullahi (Radhiyallahu Anhu) ya ce:
“Hakika ni an nuna mini daren lailatul qadri, sannan an mantar da ni shi yana goman karshe na Ramadan, dare ne da babu sanyi ko zafi a cikin sa, kuma mai haske ne”. Ibn Khuzaima.
2- Rana tana fitowa da safiyar daren fara tas.
Lokacin da aka tambayi Ubayyu Dan Ka’ab (Radhiyallahu Anhu) a kan alamomin daren lailatul qadri, sai ya ce: “Alamar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ba mu labari ita ce, rana tana bullowa a wannan rana babu haske a tare da ita”. Tirmizi.
3- Yanayi zai canza ya zama mai dadi, za a ji iska mai dadi, natsatstse”. Ibn Khuzaima da Dayalisi.
4- Samun natsuwar zuciya da kimtsuwa, da kuma farin ciki da samun jin dadin ibada (annashuwa).
5- Za ka iya ganin shi (lailatul qadr), a mafarki, kamar
yadda sahabbai suka gani.
-Ba wai za a yi mafarkin wani qwadangwame ba ne, a’a, za a iya yin mafarkin ga shi ana ibada a cikin daren.
6- Rana za ta fito babu zafi (idan lokacin zafi ne). Muslim.
Wadannan su ne alamomin da ake gane daren lailatul qadr. Amma cewar ake itatuwa za su fadi su yi sujuda, rana za ta kusanto (kasa-kasa), taurari za su kusanto (kasa-kasa), karnuka za su daina kuka, wannan tatsuniya ce aka qaga a cikin addini, wanda kuma ba gaskiya ba ne.
Allah ya datar da mu da wannan garabasa. Amin.
Usman Forlife II
08062139209

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

Create your website at WordPress.com
Get started
%d bloggers like this:
search previous next tag category expand menu location phone mail time cart zoom edit close