KIMIYYAR HADISI 1

KIMIYYAR HADISI A SAUƘAƘE 1:
GABATARWA:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.
Tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahama Muhammad, tare da iyalansa da sahabbansa, da dukkan magoya bayansa har zuwa ranar ƙarshe.
Bayan haka:
Kasancewar dukkan wani malami da zai karantar da alumma addini yana buqatar karanto musu wani ɓangare na hadisan Manzon Allah s.a.w kuma wani lokaci akan samu wasu daga cikin malamai masu ƙoƙarin bayyana matsayin hadisan da suke kafa hujja da su ta ɓangaren ingancinsu ko akasin haka. Duba da wannan lallai abu ne mai matuƙar muhimmanci ga masu bibiyar karatukan malaman addini su san tubalan da ilimin hadisi ya ginu a kansu, ta yadda za su kasance a bisa basira game da yare da laƙubban da malamai ke anfani da su wajan tantance hadisai ingattattu da waɗanda ba su inganta ba. Duk da muhimmancin wannan ilimi sai dai ba kowa ne ke bayar da lokaci na musanman ya je gaban malamai don ya karanta ya kuma fahimce shi ba, sai wanda ya san darajarsa da ƙimarsa cikin addini. Bugu da ƙari, fahimtar wannan fanni yanzu ya kan so ya zama wajibi ga dukkan musulmai musanman waxanda ke cikin alummar da shubhohi ke yawaita cikinsu ta ɓangarori daban daban na masu ƙoƙarin yaƙar addini a fakaice ko a bayyane.
Duba da wannan na ga ya zama dole kusanto da wannan ilimi ga alummarmu ta hausawa cikin harshen hausa - sannan mu fassara shi zuwa ga yaren turanci don masu fahimtar turancin bisa yardar Allah mai girma da ɗaukaka -, don ya zamo tabarau a garesu da zai yaye musu yanar da ke bisa idununsu, su fahimci wani abu na daga ƙaidojin da malaman hadisi ke bi wajan inganta hadisi ko raunana shi a ilmance.
Na sanya wa wannan littafi suna: KIMIYYAR HADISI A SAUƘAƘE.
Ina mai roƙon Allah mai girma da ɗaukaka ya sanya shi keɓance ga neman yardarsa, ya kuma sanya shi mai anfani ga al`umma mai haska hanya garesu, lallai shi majiɓincin bayinsa ne mai iko bisa dukkan komai.
Muhammad Auwal Nuhu Allemawy
29/9/1441
allemawy@gmail.com / bnnuh@yahoo.com

By:

Posted in:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started