ADDININ MUSULUNCI

NASIHA

NASIHA 2

NASIHA

HUKUNCIN ZAMAN MAKOKI !!!*

Advice

Islam

FALALAR SANIN GASKIYA, DA AIKI DA ITA.

Advice to sisters

NASIHA

 

RUWA MASU TSARKI
Shin wai ana iyayin Wankan-Tsarki ko Alwala da Ruwa mai warin Kananzir ko Petur kokuma Sabulu,??
:
Amsa
:
Dangane da hukunci akan Ruwa Mai-Tsarki kuma sai ya cuɗanya da wani abu Mai-Tsarki, Alal-Haƙiƙa Malamai Fuƙaha’u sunyi bayani dangane dacewa irin wannan Ruwa yakasune cikin halaye kamar guda uku:
:
→(1)–Hali na farko shine, idan Ruwa Mai-Tsarki ya cuɗanya da wani abu Mai-Tsarki amma bai kai ga iya jirkita Launin-Ruwan ko Ɗan-Ɗanonsa kokuma Shaƙensa ba, ta yadda babu wani canji da ya bayyana acikin Siffofi uku da ruwan yake dasu, Malamai sukace wannan Ruwan yana nan a matsayinsa na Mai-Tsarki babu wani abu da yasameshi:
:
→(2)–Hali na biyu kuma shine, idan Ruwa Mai-Tsarki ya cuɗanya da wani abu Mai-Tsarki kuma abin ya jirkita ruwan jirkitawa sosai irin wacce har yaƙwacewa ruwan asalin sunansa na ruwa, ta yadda duk wanda yaganshi bazai iya ƙiransa da sunan ruwa ba, saidai ya ambaceshi dawani suna wanda yake da alaƙa da irin abinda ya jirkita ruwan, kamar ace Misali: Zoɓo, Lemon kwalba, Kunun Zaƙi, Kumfa, Farau-Farau, Shayi, dadai sauransu, to irin wannan ruwan baya halatta ayi amfani dashi aɓangaren Ibada Ƙaulan-Wahidan,
:
→(3)–Hali na uku kuma shine, idan Ruwa Mai-Tsarki ya cuɗanya da wani abu Mai-Tsarki kuma sai ya ɗan jirkita ruwan kaɗan amma bai kai ga ya ƙwacewa ruwan asalin sunansa na ruwa ba, ta yadda duk wanda yakalleshi to zai ƙirashine da sunan ruwa, saidai wataƙila yace ruwa mai Shaƙen abu kaza, kamar Misalin ruwan da wani abu Mai-Tsarki yafada cikinsa kamar irin su:
:
Mai,
Nono,
Petur,
Kamu,
Sabulu,
Kananzir,
Za’afaran,
:
Dadai sauran makamantansu, Kokuma akadauki mazubi ko Jarkar da ake zuba wadancan abubuwa acikinta sai akayi amfani da’ita aka zuba ruwa acikinta, to idan ansauye wannan ruwan dole za’aji yana Shaƙen Kananzir ko Petur ko wani abu dabam, ammadai babu yadda za’ayi ace Kananzir dinne ko Petur aciki, dole dai yana nan amatsayinsa na sunan ruwa, Saidai ace masa ruwa mai warin Kananzir, ammadai yana nan a ruwansa, to dangane da hukuncin yin amfani da irin wannan ruwa Malamai sunyi Saɓani akai,
:
Mazhabin MALIKIYYA dakuma mafi yawa daga ciki Malamai suntafine akan cewa irin wannan ruwan sunansa Ruwa-Mai-Tsarki amma ba Mai-Tsarkakewa ba, danhaka sukace baza’ayi amfani dashiba aɓangaren da yashafi Ibada,
:
Saidai Mazhabin HANAFIYYA dakuma HANABILA suntafine akan cewa za’a’iya amfani dashi aɓangaren Ibada, hakan Mazhabin ZAHIRIYYA suma akan haka suka tafi kamar yadda Ibn-Hazm, yakawo acikin Littafinsa Al-Muhalla, sukace indai ruwa ya amsa sunansa na Ruwa-Mai-Tsarki to ya halatta ayi ibada dashi, sukace Malaman da sukace baza’ayi Ibada dashiba basu da Nassin ko daya da yace hakan daga Aʟʟαн(ﷻ) ko Aηηαвι(ﷺ), Sannan sukace tayaya za’ace wai Ruwa-Mai-Tsarki amma ba Mai-Tsarkakewa ba?? Ai indai ruwa ya amsa sunansa na Ruwa-Mai-Tsarki to shikenan yazama Mai-Tsarkakewa kenan:
:
Saidai maganar da tafi inganci cikin zantukan da Malamai sukayi itace, Ƙaulin Malaman da sukace ya halatta ayi amfani da irin wannan ruwa, saboda wasu Dalilai masu yawa da suka kalla, danhaka koda anji ruwa yana warin Kananzir to ana iyayin Wankan-Tsarki ko Alwala da wannan ruwan:
:
※(шαʟʟαнυ-тα’αʟα α’αʟαмυ)※
:
ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιℓιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα’ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:
:
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
↓↓↓
:
“المحلى بالآثار” (1/200)
:
“المجموع للنووي” (1/103)
:
“المغني لإبن قدامة” (1/20)
“”””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
“”””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””
→AMSAWA←
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
“”””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι “”lιкє””👇🏾
:
https://.facebook.com/fiqhul.ibada

Create your website at WordPress.com
Get started
%d bloggers like this:
search previous next tag category expand menu location phone mail time cart zoom edit close